Connect with us

News

INEC za ta bai wa Fintiri shaidar cin zaɓensa yau La

Published

on

Hukumar zaɓe mai zamab kanta ta kasa INEC ta ce a yau Laraba ne za ta bai wa gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da mataimakiyarsa farfesa Kaletapwa Farauta shaidar sake cin zaɓe karo na biyu.

Hukumar din ta ce za ta bai wa Fintiri da mataimakiyarsa shaidar cin zaɓen ne da misalin karfe 3 na rana.

Advertisement

Banki yayi kuskuren aikawa Me sana’ar POS Naira Miliyan 280, Inda shi kuma bai tsaya bincike ba ya fara Sharholiya

A jiya Talata ne jami’in sanar da sakamakon zaɓen jihar Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen da ƙuri’a, 430, 861.

Fintiri ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri’a, 398, 788.

Advertisement

Hukumar ɗin za kuma ta bai wa ƴan majalisar tarayya da na jihohi da aka zaɓa shaidarsu ta cin zaɓe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending