Connect with us

News

Tallafin Biliyan 180: Gwamnoni Ba Abin Yadda Bane Da Kuɗaɗe. NLC 

Published

on

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) Joe ajero

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta soki shirin mika Naira biliyan biyar na tallafi ga gwamnonin jihohi 36 a Najeriya.

Kungiyar ta ce gwamnoni ba abin yarda ba ne inda su ka ce gwamnonin kawai za su ba wa ‘yan siyasa ne a jihohinsu.

Advertisement

Wakilin Jaridar Leadership Ya Rasu A Kano.

A baya dai an sha ba wa gwamnonin jihohi irin wadannan kudade don rabawa talakawa amma kuma su ka mamaye kudin tare da ba wa wasu ‘yan tsiraru da su ke da alaka da su.

A ranar Alhamis 17 ga watan Agusta, Gwamnatin Tarayya ta sanar da ware Naira biliyan biyar ga jihohi 36 na kasar da kuma ware tireloli 180 na shinkafa don rage radadin yunwa.

Advertisement

Gwamnatin Tarayyar ta ware Naira biliyan 180 don rabawa jihohi 36 Naira biliyan biyar don rage radadin cire tallafi.

Tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi, ‘yan kasar su ka shiga mawuyacin hali.

Advertisement

Cire tallafin ya jawo hauhawan farashin kayayyaki da kuma tsadar mai din da ta jefa ‘yan Najeriya cikin wani irin yanayi

Kungiyar NLC a kwanakin baya ta yi zanga-zanga kan hauwawan farashin kaya a kasar da kuma neman Tinubu ya gyara matatun mai a kasar nan.

Advertisement

Wasu da dama na ganin cewa, bai wa gwamnoni irin wadannan kudade zai sanya su raba ma yan jam’iyyar su ne maimakon ainihin masu bukatar tallafin kamar yadda aka sha zargi a baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending