Connect with us

News

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaba Tinubu da ya dakatar da ministocina daga karɓar fansho.

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Ƙunuiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya gaggauta dakatar da tsofin gwamnonin ƙasar dake rike da mukamin minista daga karɓar fansho a Jihohinsu.

Advertisement

Kazalika kungiyar ta ce tilas ne tsofin gwamnonin su jingine batun karbar motocin alfarma da kuma sauran alawus alawus da suke samu daga jihohin nasu.

Buhari ya jajanta wa iyalan sojojin da aka kashe a Neja.

Har wa yau kungiyar ta bukaci Tinubu da ya umarci ministocin nasa da su maido da fansho da kuma alawus alawus da suka karba tun bayan barinsu kujerar gwamna zuwa ga baitilmalin jiha.

Tsofin gwamnonin dake riƙe muƙamin minista a halin yanzu sun haɗa da Badaru Abubakar da Nyesom Wike da Bello Matawalle da Adegboyega Oyetola hadi da David Umahi.

Advertisement

Sauran sun haɗa da Simong Lalong da Atiku Bagudu gami da Ibrahim.

Cikin wata wasiƙa da SERAP ta fitar ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun mataimakin Daraktanta Kolawole Oluwadare ta ce abinda tsofin gwamnonin ke yi na karɓar fansho bayan an naɗa a kujerar minista ya saɓawa kundin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa gyaran fuska.
“Dakatar da wadannan gwamnoni daga karɓa fansho a jihohin aikin al’umma ne domin hakan zai sa al’umma su mora ba wai kawai ga ƴan tsirarun yan siyasa ba.”
Dokar ƙasa ta haramtawa masu riƙe da mukaman gwamnati aikata ba daidai ba ciki har da ƙarbar fansho daga jihohinsu, wannan zamba ne cikin aminci.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *