News
Jami’in Hukumar DSS Ya Soka Wa Tsoho Wuka Kan Naira N3,000
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ana zargin wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ya soka wa wani dattijo mai shekara 62 wuka kan Kudi Naira 3,000.
Rahotanni na nuni da cewa jami’in na DSS ya soka wa mutumin wuka ne saboda taƙaddamar da suka yi kan kuɗin wutar lantarki Naira 3,000.
Dattijon mai suna Omoshola Oludele, shi ne kiya-tekan gidan da jami’in da DSS ke zaman haya a unguwar Tinumola da ke garin Osogbo, Jihar Osun.
Shaidu sun ce kiya-tekan ya je tattara kuɗin wutan gidan ne, amma jami’in ya ki biya, lamarin da ya kai su ga cacar baki, har jami’in ya caka masa wuka.
Wani ganau mai suna Tosin Moronkola, ya ce jami’in na DSS ya yi wa Mista Oludele mummunan rauni a kwankwaso, kuma an asibiti domin yi masa magani.
Mazauna unguwar sun bukaci ’yan sanda da sauran hukumomin da ke da alhaki su ɗauki mataki a kan jami’in na DSS domin guje wa aukuwar irin haka a nan gaba.
Wani babban jami’in DSS ya shaida wa wakilin jaridar Daily Trust cewa hukumar za ta bincika lamarin kuma za ta hukunta wanda ake zargin idan ta same shi da laifi.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
