News
YIN TALLACE TALLACE HARAMUN NE A BIRNIN ABUJA. Cewar ministan babban birnin wike
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ministan babban birnin tarayyan, ya sanar da haramta tallace-tallace a bakin tituna a Abuja, yana mai cewa mutanen da ke sayar da masara, ‘yan dako, da sauran sana’o’i akan titi ke haddasa rashin tsaro da jawo aikata laifuka a babban birnin tarayyar,
Hikima Media News ta ruwaito Wike ya kara da cewa duk da ya san ana fama da tsadar rayuwa amma hakan bai kamata ya zama uzuri ga rashin bin doka da oda a babban birni ba
Fargaba da firgici ya mamaye mazauna birnin musamman Masu matsakaita da karamin karfi tin bayan rantsar da tsohon gwamnan na jihar Rivers a matsayin saban ministan babban birnin da shugaba tinubu yayi
“Tsauraran matakan da ministan ke dauka suna tina mana lokacin mulkin El-rufa’i” inji wani mazaunin yankin
Sai dai a firar da hikima tayi da Dr umar Muhammad wani Mai sharhi akan lamura a kaduna yace
“Tabbas tsaurarawa na kawo gyara kamar yadda ta faru a lokacin mulkin El-rufa’i amma wannan yanayin ya banbanta ana cikin matsanin Hali, ina ganin hana sana,o,in shine zai haifar da rashin tsaran maimakon maganceshi akwai bukatar wike ya sake nazari akan mataki”
Fatan hikima Media News shine Allah ya saukaka mana la
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
