Connect with us

News

Rundunar ’Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Bindiga Ɗauke Da Makamin Roka A Jahar Yobe

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rundunar ’Yan sandan a yankin Karasuwa na Jihar Yobe sun cafke wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, dauke da makamin roka, wanda aka fi sani da RPMG Motar.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim ya bayyana mutane biyun da aka kama sun shigo Jihar Yobe ne daga Zamfara.

Advertisement

Sama da ‘yan Najeriya miliyan 27 ne ba sa amfani da yanr gizo

Dungus ya ce, “na farko da aka kama ne ya bayyana cewa dayan ne mai yin safarar makamai ga ’yan ta’adda a Zamfara, shi ne ’yan sanda suka bi sawunsa har yankin Maradun a Jihar ta Zamfara suka kamo shi, ana kuma ci gaba da binciken wadanda ake zargin.

“An kama wanda ake zargin na farko yana tuka mota Toyota Hiace mai dauker mutum 18 a Karasuwa, sakamakon rahoton sirri da aka samu a lokacin da yake kokarin karbar wannan makami na roka (RPMG),” in ji sanarwar da jami’in ya fitar.

Dungus ya ce bincikensu ya gano wadanda ake zargin suna kai wa ’yan bindiga makamai ne a jihohin Zamfara, Kano, Neja, Kaduna, Yobe da dai sauransu.

Advertisement

Ya kara da cewa Kwamishanan ’yan sandan jihar, Garba Ahmed ya yi alkawarin ci gaba da karfafa gwiwar jami’an runduar gwiwa domin ci gaba da zakulo ’yan ta’adda da kuma yin maganin su.

Ya shawarci jama’a da su ci gaba da baiwa ’yan sanda bayanai masu amfani da zai kai ga damke masu laifin da ke cikin al’umma.

Wani labarin kuma Sama da ‘yan Najeriya miliyan 27 ne ba sa amfani da yanr gizo

Advertisement

 

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

Advertisement

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Advertisement

 

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

 

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *