Connect with us

News

Da Dumi-Dumi: Kotun Sojoji Ta Yankewa Manjo Janar Hukuncin Daurin Shekaru 7 A Gidan Yari

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Yanzu haka dai wata kotun sojin Najeriya ta musamman da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta yanke wa tsohon Manajan Darakta na rukunin, Nigerian Army Properties Limited, Manjo Janar Umaru Mohammed, hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.

Baya da haka kotun ta kuma umarce shi da ya mayar da tsabar kudi dala 2,178,900 da kuma Naira biliyan N1.65bn ga kadarorin Sojoji da NAPL.

Advertisement

Ƴan bindiga sun yi awon-gaba da ɗalibai huɗu na jami’ar jihar Nasarawa

An gurfanar da Mohammed ne a kan tuhume-tuhume 18 da suka hada da jabun takardu, karkatar da kudade, da kuma hada baki da sauransu.

Ko da yake manjo Janar din ya ki amsa dukkan zarge-zargen, amma kotun ta same shi da laifuka 14.

Advertisement

A wani labarin kuma Ƴan bindiga sun yi awon-gaba da ɗalibai huɗu na jami’ar jihar Nasarawa

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending