Connect with us

News

An Yi Arangama Tsakanin Jami’an NDLEA Da ‘Yan Sanda Yayin Da Aka Kama Matar Insfekta Da Wiwi A  Jahar Kogi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Jami’an Rundunar ‘yan sanda da jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar Kogi sun kwashi dauki ba dadi akan matar wani Insfektan dan sanda da aka kama ta da buhun tabar wiwi da kuma wasu miyagun kwayoyi.

Rikicin ya faro asali ne bayan da jami’an hukumar ta NDLEA suka kama matar Sufetan da ake zargi dauke da tabar wiwi, a cikin wata mota mallakar mijinta a ranar litinin.

Advertisement

Kasar Mali ta lallasa Kasar Saudiyya da ci 3 da 1

Shahara reporters rawaito cewa wasu Majiyoyi sun bayyana cewa an kama matar ne a lokacin da take raraba kayayyakin.

 

Advertisement

Sai dai kuma da jami’an hukumar NDLEA suka yi yunkurin tafiya da ita sai wasu ‘yan sanda suka nemi dakile lamarin wanda hakan ya jawo barkewar rikici tsakanin su.

 

Advertisement

Duk da kokarin da jami’an ‘yan sanda suka yi na dakile kama matar hakan bai yiwu ba har sai da jam’ian hukumar ta NDLEA su ka yi nasarar cafketa zuwa ofishin su da ke Lokoja domin ci gaba da bincike.

A wani labarin kuma Kasar Mali ta lallasa Kasar Saudiyya da ci 3 da 1

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending