News
Naira 50,000 Ake Biya Na Duk Lokacin Da Na Yi Safarar Makamai Zuwa Wurin ‘Yan Bindiga – Aisha Abubakar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata mata da jami’an rundunar ‘yan sanda suka kama da carbin alburusai 550 na bindigar AK47 ta bayyana cewa ana biyan ta Naira dubu hamsin duk lokacin da ta yi safarar alburusai zuwa ga ‘yan bindiga a jihar Katsina.
Matar, mai suna Aisha Abubakar, ‘yar shekara 25, ta fada komar rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a tsakanin Kaduna zuwa Zaria yayin da take kan hayarta ta zuwa Katsina daga garin Loko a jihar Nassarawa a ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni, 2024.
Muhimman Abubuwa Bakwai Da Shugaba Tinubu Ya Amince Da Su Bayan Ganawarsa Da Gwamnonin Nijeriya
Aisha ta yi magana da manema labarai yayin da rundunar ‘yan sanda ta yi bajakolin masu laifi a hedikwatar ta ranar Alhamis.
“Jami’an ‘yan sanda sun kama ni da alburusai. Da farko wani ne mai suna Wawo ya kawo min buhun taki ya ce na tura Katsina ta hanyar bawa wani direba.
“A karo na biyu kuma da kaina na je har Katsina na kai makaman. A zuwana na uku ne ‘yan sanda suka kama ni. Ana biya na N50,000 kowacce tafiya,” a cewar ta.
Rahotanni na nuni da cewa a Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar gano alburusan ne a wani binciken kayan matar da aka yi.
Da farko wacce ake zargin ta musanta aikata safarar kafin daga baya ta amince da aikata wannan laifi.
Kwamishinan ‘yan sanda, Ali Audu Dabigi, ya bayyana cewa bayanan da Aisha ta bayar dangane da masu bata makamai ya kai ga, ya zuwa yanzu, an kama wasu mutane biyu.
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News7 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
