Connect with us

News

Mahaifin Da Ake Zargin Ya Kashe Jiririnsa Ɗan Kwana 3 Ya Shiga Hannun Ƴansanda

Published

on

IMG 20241109 WA0027 1024x512

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Aliyu Yaro, matashi mai shekara 19, bisa zargin kashe jaririnsa ɗan kwanaki uku da haihuwa.

Yaro, mazaunin unguwar Kwacham a Mubi ta Arewa, ya amsa laifin kuma ya jagoranci Ƴansanda zuwa wurin da aka binne jaririn.

Hukumar JSC Ta Kano Ta Dauki Matakin Ladabtarwa Kan Ma’aikatan Shari’a Guda Takwas   

LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa, Yaro ya aikata wannan aika-aikar ne bayan mahaifiyar jaririn, ta nemi ya ɗauki nauyin kulawa da shi. Yaro ya je gidan mahaifiyar jaririn da daddare, ya tura ta tafi nemo ruwa, sannan ya ɗauke jaririn daga baya ya binne shi a yankin Girpata a Mubi.

Kwamishinan Ƴansandan Jihar, CP Morris Dankombo, ya nuna damuwarsa kan wannan lamari, tare da bayar da umarnin miƙa lamarin zuwa Sashen binciken manyan laifuka don ci gaba da bincike da kuma gurfanar da wanda ake zargin gaban Kuliya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending