Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa ’Yan China Huɗu Hukuncin Zaman Gidan Kaso Na Shekaru Biyar

Published

on

Yan china

Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, jihar Filato, ta yanke wa wasu ’yan kasar China huɗu hukuncin zaman gidan kaso na shekara biyar kowannensu, bisa laifin haƙar ma’adanai ba tare da izini ba.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ce ta gurfanar da su gaban kotu, inda ta ce an kama su ne a watan Maris a wani filin haƙar ma’adanai da ake kira JLM Mining da ke kusa da Barikin Ladi.

Matsalar Ruwan Sha: Matan Aure Da ’Yan Mata Na Kwana Waje Don Neman Ruwa A Kauyukan Kano

Waɗanda abin ya shafa su ne Liang Quin Yong, Wang Huajie, Zhong Jiajing, da Long Kechong.

EFCC ta ce an kama su ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukan su da ake zargin ba bisa ƙa’ida ba suke gudanarwa.

Da aka gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Dorcas V. Agishi, dukkaninsu sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi.

Lauyoyin EFCC, M.O. Arumemi da F.A.I Asemebo, sun roƙi kotu ta ɗauki matakin da ya dace da irin laifin da suka aikata.

Advertisement

A hukuncin da kotun ta yanke, ta ɗaure su shekara biyar kowannensu tare da umarnin biyan tarar Naira miliyan ɗaya kowanne.

Baya ga haka, kotun ta bayar da umarnin a kore su daga Najeriya bayan sun kammala zaman gidan kaso, tare da haramta musu sake shigowa ƙasar. Haka kuma, za a kwace duk kadarorin da suka mallaka a ƙasar, a mika su ga Gwamnatin Tarayya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending