Connect with us

News

Jami’ar Northwest Ta Bai Wa Dalibai Damar Biyan Kuɗin Makaranta A Rarrabe

Published

on

Gwamnatin Kano ta dawowa da jami'ar Northwest sunanta na asali

Biyo bayan korafe-korafen da ɗalibai suka shigar sakamakon karin kuɗin makaranta da aka yi a Jami’ar Northwest da ke Kano, hukumar jami’ar ta amince da tsarin biyan kuɗin makaranta a rarrabe, domin rage wa ɗalibai nauyin da karin ya janyo.

Shugaban ɗaliban jami’ar, Ambasada Khaleed Hassan Hudu, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da PREMIER RADIO, inda ya ce matakin ya biyo bayan doguwar ganawa da suka yi da shugabancin jami’ar domin lalubo hanyoyin da za su saukaka wa ɗalibai.

Advertisement

IFAB Za Ta Fara Aiwatar Da Sabbin Dokokin Ƙwallon Ƙafa A Kakar 2025/26

Ya ce, “Mun gudanar da doguwar tattaunawa da shugabannin jami’ar, inda muka bayyana musu irin halin kunci da ɗalibai ke fuskanta. Alhamdulillah, sun fahimci matsin da muke ciki, suka amince da tsarin biyan kuɗi a rarrabe.”

Ambasada Khaleed ya jaddada cewa, wannan mataki na daga cikin muhimman nasarori da ƙungiyar ɗalibai ta cimma a wannan lokaci mai cike da ƙalubale, musamman duba da yadda ake fama da hauhawar farashi da matsin tattalin arziki a fadin ƙasa.

Advertisement

A makonni da suka  gabata ne dai jami’ar ta sanar da karin kuɗin makaranta, wanda hakan ya jawo tashe-tashen hankula daga ɓangaren ɗalibai da iyaye, inda da dama suka nuna damuwa da yadda za su iya biya a lokaci guda.

“Mun san ba sauki ba ne, amma dole ne mu ci gaba da jajircewa wajen kare muradun ɗalibai. Wannan mataki zai ba da damar ci gaba da karatu ba tare da tangarda ba,” in ji shugaban ɗaliban.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending