News
Sojoji Sun Cafke Ƴan Bindiga, Sun Ƙwato Makamai A Kaduna Da Filato
Sojojin Runduna ta 3 ƙarƙashin Operation SAFE HAVEN sun kama wani da ake zargin ɗan bindiga ne a Katsit, Zangon Kataf, da ke jihar Kaduna.
Wanda aka kama yana sanye da kayan soji, kuma ana zargin yana shirin kai hari da sace jama’a a yankin kafin a cafke shi.
Shirin Dangote Na Raba Mai Kyauta Zai Kassara Mu – Inji Dallalan Mai
An ƙwato bindigar AK-47, makami, harsashi 3, kwankon harsasai 7, katin ‘yan sa kai na bogi, waya da katin ATM guda biyu.
Sojojin sun miƙa wanda ake zargin hannun hukumomi domin ci gaba da bincike da daukar matakin shari’a a kansa.
A wani samame daban, sojoji sun kai farmaki maɓoyar masu safarar makamai a Kwanar Lauje, ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato.
Kodayake barayin sun tsere kafin isowar sojoji, amma an gano bindigu, harsashi 300 da kayan haɗa AK-47 da makaman harbo jirgin sama.
Har ila yau, sojoji sun ƙwato babur da ɓarayin suka bari a wajen; yayin da bincike ke ci gaba da gudana don kamo waɗanda suka tseren.
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News17 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
