Connect with us

News

‎EFCC Za Ta Gurfanar da Kwamishinan Kuɗi Na jihar Bauchi Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 4.6

Published

on

Dr Yakubu Adamu e1765640415332 474x430 (1)
Spread the love

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da cewa za ta gurfanar da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Dakta Yakubu Adamu, a gaban kotu saboda zargin badakalar kuɗi da ya kai Naira biliyan 4.6.

‎EFCC ta ce za a gurfanar da Dakta Adamu tare da wani kamfani mai suna Ayab Agro Products and Freight Company Ltd a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Emeka Nwite, kan tuhume-tuhume shida da suka shafi badakalar kuɗi.

Gwamnan Gombe Ya Kori Hadimansa 4 Kan Cin Zarafin Kansila

‎An shirya a yi zaman kotu a ranar Litinin, amma shari’ar ba ta ci gaba ba sakamakon rashin halartar lauyan EFCC da wadanda ake kara, duk da cewa lauyoyin masu kare kansu sun hallara.

‎ Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa 24 ga Disamba, 2025, domin ɗaukar bayanan .

Advertisement

‎Rahotanni sun nuna cewa ana zargin Dakta Adamu, wanda a baya ya riƙe mukamin Manajan reshen Polaris Bank a Bauchi, da haɗa baki da wasu mutane biyu wajen karkatar da kuɗaɗen da aka bayar a matsayin rancen sayen babura domin gwamnatin Jihar Bauchi, tsakanin Yuni zuwa Disamba 2023.

‎EFCC ta ce an bai wa kuɗaɗen ne ta hannun Polaris Bank, ƙarƙashin hujjar sayen babura ta kamfanin Emmanuel Asomugha General Enterprises, amma ba a kawo kayan ba, abin da ya saɓa wa dokar hana badakalar kuɗi ta shekarar 2022.

‎A cewar tuhume-tuhumen, wani ɓangare na kuɗaɗen—har Naira miliyan 165.9—an tura shi zuwa asusun Ayab Agro Products and Freight Company Ltd, wanda ake zargin wani ɓangare ne na kuɗaɗen da aka samo ta hanyar da ba ta dace ba.

‎Hukumar ta ce laifukan sun saɓa wa Dokar Hana da Hukunta masu laifin badakalar Kuɗi ta 2022, wadda ke ɗauke da hukunci mai tsauri. Har yanzu, ba a ji ta bakin gwamnatin Jihar Bauchi ko Dakta Yakubu Adamu ba kan wannan batu.

Advertisement

 

 

SOLACEBASE

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *