News
‘’Yan Ta’adda Sun Fara Amfani Dana’urar POS Wajen Karɓar Kuɗin Fansa’
Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi kan yadda ’yan ta’adda ke ƙirƙirar sabbin hanyoyi, ciki har da amfani da na’urar POS, wajen karɓar kudin fansa da kuma kauce wa bin sahunsu.
Haka kuma ta ce hukumomin tsaro na Najeriya suna aiki tare da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin ganowa da kuma rufe asusun da ’yan ta’adda da kungiyoyin masu laifi ke amfani da su wajen yada ayyukansu da tara kuɗi.
EFCC Za Ta Gurfanar da Kwamishinan Kuɗi Na jihar Bauchi Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 4.6
Daraktan Cibiyar Kasa ta Yaki da Ta’addanci (NCTC), Manjo-Janar Adamu Laka, ne ya bayyana haka ga ’yan jarida ranar Talata a hedikwatar cibiyar da ke Abuja yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara ta 2025.
Babban jami’in sojan ya nuna damuwa cewa biyan kudin fansa ya ci gaba da zama babbar hanyar samun kuɗi ga ’yan ta’adda, inda ake ta amfani da masu aiki da POS wajen sarrafa kuɗin.
Ya ce a lokuta da dama, ana tura kudin fansa zuwa asusun masu POS, sannan su fitar da kuɗin ga masu garkuwa da mutane, abin da ke sa bin diddigin kuɗin ya zama mai wahala.
“Za ka ga an canja wurin kuɗin daga hannun ’yan ta’adda, amma idan aka bincika asusun, na mai POS ne. Masu garkuwa da mutane suna bayar da lambar mai PoS, sai a tura kuɗin, daga nan su je su karɓa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun ƙara ƙaimi wajen bin diddigin kudin fansa, kama wadanda ke da hannu, da kuma katse hanyoyin samun kuɗin ta’addanci, sai dai ya ce ba za a iya bayyana cikakkun bayanan dabarun aiki ba saboda tsaro.
Laka ya kuma ce an kama tare da gurfanar da mutane da dama a gaban kotu dangane da biyan kudin fansa da kuma masu tallafa wa ta’addanci da kudi.
Ya ƙara da cewa kwace dukiya da kuma kama kadarori na daga cikin matakan da Najeriya ke ɗauka wajen bin ƙa’idojin duniya na yaki da safarar kuɗi da kuma kuɗin ta’addanci.
Ya lissafa TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X a matsayin wasu daga cikin kafafen da ’yan ta’adda suka fi amfani da su wajen yada ayyuka, nuna abin da suka kwace, da kuma sadarwa da magoya baya.
A cewarsa, hukumomin tsaro sun yi tarurruka da kamfanonin kafafen sada zumunta domin dakile rubuce-rubuce da shafukan da ke barazana ga tsaron ƙasa.
Ya ce dabarun ’yan ta’adda na ci gaba da sauyawa, ciki har da amfani da sunayen ƙarya da asusun da ba a tabbatar da su ba, inda ya ƙara da cewa hukumomin tsaro suna daidaita dabarunsu a kai a kai domin dakile irin waɗannan abubuwan.
