Advertisement

Ana sa ran dan wasan tsakiya na Barcelona da Holland Frenkie de Jong, ya ci gaba da zama a Nou Camp a bazaran nan duk da sha’awarsa da Manchester United da Chelsea da kuma Liverpool ke yi. (CBS Sports)

Liverpool na dubu yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na Sheffield United da Norway, Sander Berge mai shekara 24. (Yorkshire Post)

Advertisement

Leicester da Everton na son gaggauta zawarcin dan gaban Al Hilal, Matheus Pereira dan Brazil mai shekara 26. (Sun)

Valencia na da kwarin gwiwa za ta kasa Real Sociedad wajen daukar Edinson Cavani, kuma ta shirya bashi kwantiragin shekara biyu. (Fabrizio Romano)

Advertisement

Dan bayan Tottenham da Sifaniya, Sergio Reguilon mai shekara 25, ya shirya tafiya Atletico Madrid aro, amma kuma yarjejeniyar ta ce ba damar sayen shi. (Fabrizio Romano)

Dan wasan tsakiya na Spurs da Ingila Harry Winks, na dab da tafiya Sampdoria bayan da ya jira ko zai samu wata kungiya ta Premier da za ta dauke shi. (Evening Standard)

Advertisement

Chelsea ta yanke shawarar cewa dan bayanta Trevoh Chalobah, dan Ingila ba zai bar kungiyar ba a wannan bazara duk da cewa ya tattauna da Inter Milan da AC Milan da RB Leipzig, domin tafiya aro. (Fabrizio Romano)

Chelsea na fatan doke Tottenham da Crystal Palace wajen sayen matashin dan bayan Peterborough na Ingila, Ronnie Edwards, mai shekara 19. (Football Insider)

Advertisement

Spezia za ta dauki aron dan wasan tsakiya na Wales, Ethan Ampadu mai shekara 21, daga Chelsea tare da damar sayensa a kan kudin da ya kai Fam miliyan 12.7 (Fabrizio Romano)