Sports
Chelsea za ta yi babban cefane, Ronaldo zai koma Napoli
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Chelsea za ta kara dagewa wajen ganin ta yi nasarar sayo Pierre-Emerick Aubameyang, daga Barcelona, idan ta kammala cinikin Fam miliyan 70 na dan bayan Leicester Wesley Fofana, dan Faransa mai shekara 21.
Kungiyar ta Stamford Bridge tana kuma son sayen matashin dan gaba na gefe Anthony Gordon na Everton, dan Ingila mai shekara 21 a wannan makon. (Guardian)
Ita kuwa Tottenham na tattaunawa ne domin karbar aron dan gaba na gefe na Leeds United da Wales Daniel James, kafin ranar Alhamis da za a rufe kasuwar ‘yan wasa da karfe 11 na dare agogon Najeriya. (Fabrizio Romano)
Haka kuma, Spurs din sun kara taso da bukatarsu ta ganin sun sayi gwanin dan wasan tsakiya na Atletico Madrid, ko’ina-da-ruwanka, Yannick Carrasco, dan Belgium mai shekara 28. (Telegraph – subscription required
Cristiano Ronaldo zai iya barin Manchester United zuwa Napoli a wannan makon.
Sau daya aka fara sanya gwarzon dan wasan na Portugal a wasannin United hudu na Premier na bana. (Metro)
Aston Villa na matukar sha’awar daukar kociyan Brighton Graham Potter a matsayin wanda zai iya maye gurbin Steven Gerrard, wanda ya jagoranci kungiyar ta yi rashin nasara a wasanninta uku cikin hudu na farkon kakar nan. (Football Insider)
Newcastle na sha’awar dan wasan tsakiya na Chelsea Tiemoue Bakayoko, dan Faransa mai shekara 28, wanda AC Milan ta karba aro shekara biyu. Nottingham Forest ma na bukatarsa. (Calciomercato – in Italian)
Crystal Palace ta gabatar da tayin Fam miliyan 27 a kan dan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher, na Ingila mai shekara 22, wanda ya taka rawar gani sosai a zaman aron da ya yi a kungiyar a kakar da ta gabata ta 2021-22. (Times – subscription required)
Dan bayan Arsenal Hector Bellerin, dan Sifaniya mai shekara 27, ka iya tafiya Real Betis, inda ya je aro a kakar da ta gabata.
Rabon da Bellerin ya taka wa Gunners din leda tun watan Mayu na 2021. (Estadio Deportivo – in Spanish)
Dan wasan tsakiya na Barcelona da Holland Frenkie de Jong, zai ci gaba da zama a kungiyar duk da yadda aka yi ta danganta shi da tafiya Manchester
United ko Chelsea a lokacin kasuwar ‘yan wasa. (Football Espana)
Sai dai kuma duk da haka an ce De Jong din zai je Ingila kafina rufe kasuwar, abin da ya sa ake yada jita-jita kan ci gaba da zamansa a Barca.(Mirror)
Aston Villa da Wolves na sha’awar sayen dan bayan West Ham Craig Dawson, dan Ingila mai shekara 32. (Sun)
Juventus za ta yi kokarin ganin ta sayi dan wasan tsakiya na Aston Villa Douglas Luiz, dan Brazil mai shekara 24, idan har ta kasa cimma yarjejeniya da Paris St-Germain a kan Leandro Paredes, dan Argentina mai shekara 28. (Sky Sport Italia – in Italian)
Dan bayan Liverpool da tawagar Holland ta ‘yan kasa da shekara 21 Sepp van den Berg, na shirin tafiya Schalke aro. (The Athletic – subscription required)
Leicester City kuwa na tattaunawa da Schalke domin sayen dan wasan tsakiya na Morocco Amine Harit, mai shekara 25. (Sky Sports)
Fulham ta cimm yarjejeniya da Paris St-Germain kan sayen dan bayanta Layvin Kurzawa, dan Faransa mai shekara 29.
Haka kuma Fulham din na kokarin sayen dan gaba na gefe na Roma Justin Kluivert, dan Holland mi shekara 23. (Mail)
