Sports
Man Utd za ta raba gari da Ronaldo, Mudryk ya yi kasuwa, City za ta san matsayinta kan Silva
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Watakila Manchester United ta kawo karshen kwantiraginta da Cristiano Ronaldo sakamakon cikakkiyar hirar da ya yi da Piers Morgan, sai dai kungiyar za ta saurari hirar gaba daya tukuna kafin ta yanke hukunci a kan ci gaba da zaman dan wasan na Portugal a Old Trafford.
Dan wasan zai iya tafiya Chelsea bayan da aka bayar da rahotannin cewa ya so tafiya a bazara amma kociyan kungiyar da aka sallama Thomas Tuchel, ya hana.
Manchester United ta bi sahun Arsenal wajen zawarcin dan wasan gaba na gefe na Shakhtar Donetsk da Ukraine Mykhaylo Mudryk, inda aka ce kociyan United, Erik ten Hag na sha’awar matashin mai shekara 21 tun yana kociyan Ajax.
A wata hira da shafin YouTube na matar dan bayan Arsenal Oleksandr Zinchenko, Vlada Sedan, Mudryk ya ce ya kwammace ya je Arsenal inda za a rikasanya shi a jerin ‘yan wasa na farko maimakon ya je ya rinka zama a benci a Real Madrid.
Sai dai ya ce yana son tattaunawa da kociyan Arsenal Arteta kafin ya yanke shawara kan makomarsa.
Liverpool na sha’awar matashin dan wasan tsakiya na Las Palmas Alberto Moleiro, wanda rahotanni ke cewa Barcelona da Manchester City ma na sha’awar dan Sifaniyar mai shekara 19.
Roma za ta iya sauraron tayi a kan dan wasanta Tammy Abraham, dan Ingila.
Tottenham ta tura masu yi mata farautar ‘yan wasa domin su je su sa ido a kan dan wasan Faransa na gaba Marcus Thuram, mai shekara 25 a Borussia Monchengladbach, da kuma dan Kamaru Youssoufa Moukoko, matashi mai shekara 19, a Borussia Dortmund, a lokacin wasan Bundesliga na ranar Juma’a tsakanin kungiyoyin biyu.
Ita ma Liverpool da Arsenal na sha’awar Thuram, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kaka kuma ana danganta shi da tafiya Bayern Munich.
Chelsea na da kwarin guiwar cewa ta cimma yarjejeniya da dan gaban RB Leipzig Christopher Nkunku kuma dan Faransar mai shekara 25 zai koma kungiyar a watan Janairu ko bazara.
Manchester City na shirin tattaunawa da wakilin dan wasanta na tsakiya Bernardo Silva a lokacin wasan Kofin Duniya domin sanin yadda za ta yi da makomar dan wasan.
Zakarun na Premier sun san cewa dan wasan na Portugal na son tafiya Barcelona kuma kungiyar ba za ta hana shi ba idan an yi mata tayi mai kyau.
Dan bayan Leeds United Cody Drameh, dan Ingila mai shekara 20, na daukar hankalin Newcastle United, da Lille da Borussia Dortmund da kuma Bayer Leverkusen.
Dole ne tsohon kociyan Chelsea, Thomas Tuchel ya bar Birtaniya a watan Disamba, saboda dokokin yarjejeniyar fitar kasar daga Tarayyar Turai sakamakon Chelsea ta sallame shi.
To amma mataimakansa biyu, Zsolt Low da Benjamin Webber, wadanda kusan har yanzu kwantiraginsu na nan a hukumance ka iya ci gaba da zama a kasar.
BBC
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News7 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
