Connect with us

News

Majalisar Kano Ta Amince Da Karin N55bn A Kasafin Kudin 2022 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da karin naira biliyan 55 a kasafin kudin jihar na bana.

Advertisement

 

Amincewar ta zo ne bayan karatu na uku da aka yi wa kudirin jim kadan bayan amincewa da rahoton da shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na majalisar, Alhaji Abba Ibrahim, ya gabatar yayin zaman da shugaban majalisar, Alhaji Hamisu Chidari ya jagoranta.

Advertisement

 

Tinubu ya gana da ƙungiyar kiristoci ta CAN

Ibrahim ya ce an yanzu an kara Kasafin Kudin na bana zuwa sama da Naira biliyan 276, bayan bukatar Gwamna Abdullahi Ganduje ya gabatar na bunkasa ci gaban jihar.

Advertisement

 

Dan majalisar ya bayyana cewa, an kara karin kasafin kudin daga Naira biliyan 43 zuwa naira biliyan 55 domin gudanar da ayyukan Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta jihar (SUBEB) da sauran ayyuka.

Advertisement

 

A cewarsa, tare da amincewa da karin Kasafin Kudin, abin da ake kashewa manyan ayyuka a yanzu ya kai Naira biliyan 160, yayin da abin da ake kashewa na yau da gobe ya kai Naira biliyan 115.

Advertisement

 

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Disamba domin ba da damar kare kudurin kasafin kudin.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending