News
Ronaldo ya sha naushi a fuska a wasansu da PSG
DAGA HASSAN KHALID HAMZA
Christiano Ronaldo ya sha naushi a fuska, amma duk da haka ya jefa kwallaye biyu a wasan sada zumunta da sabuwar kungiyarsa ta Al Nassr ta yi da PSG a birnin Riyadh na Saudiya a yau.
Mai tsaren ragar PSG, Keylor Nava, shi ne ya naushi Ronaldo da dungulalliyaar hannu, lamarin ya sa alkali ya ba shi bugun fanariti wanda Ronaldo din ya zura a raga.
Koda yake PSG ce ta samu nasara da kwallaye 5-4 a wasan wanda ya sake hada Ronaldo da tsohon abokin hamayyarsa a duniyar tamola, wato Lionel Messi na PSG.
Messi da Kylian Mbappe dukkaninsu sun jefa kwallo a raga a yayin fafatawar, yayin da Neymar ya barar da bugun fanariti.
Daga cikin ‘yan kallo da suka halarci filin wasan na Sarki Fahad mai daukar nauyin mutane dubu 69, har da wani attajirin Saudiya mai rikunin gidaje da ya biya Dala miliyan 2.6 domin sayen tikitin kallon wasan kai tsaye.
-
News2 days ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News4 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News7 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
