News
Yan Sandan kano cafke wasu matasa biyu da laifin yin garkuwa yara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu matasa biyu da zargin yin garkuwa da wasu yara da suke anguwar Bachirawa dake ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano
Jam’i’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yammacin Talatar nan,
Inda ya ce tuni jami’an su suka kuɓutar da yaran a hannun masu garkuwa da su ɗin.
“Mun samu korafin ne a ranar 26 01 2023 daga wasu mutane da suka yi kan cewar ƴaƴansu Umar Isyaku ɗan shekaru 3, da kuma Aliyu Auwal ɗan shekaru 4, an yi garkuwa da su tare da neman Naira Miliyan 20, a matsayin kuɗin fansa”
Advertisements
