News
A Cikin Ramadan Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Miyagun maharan yan bindiga sun kai mummunan hari ga matafiya a titin Kaduna zuwa Abuja a wani gari da ke kusa da Kagarko.
Shuaibu Yahaya, wani mazaunin garin wanda gidansa ke kusa da inda abin ya faru ya ce maharan sun fasa tayoyin motoccin matafiyan ne kafin suka rika bi suna kwashe su zuwa daji Madakin Jinjila,
Samaila Babangida shima ya ce an kira ne daga garin Kagarko an sanar da shi afkuwar harin amma ba zai iya tantance adadin mutanen da abin ya shafa ba
An sace matafiya da dama bayan yan bindiga sun bude wa motocci wuta a garin Iche, mai nisanta wasu yan kilomita daga garin Kagarko da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, wani mazaunin unguwar, Shuaibu Yahaya, ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 7 na yammacin ranar Laraba jim kadan bayan an sha ruwa.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
