News
Kungiyar ‘yan jaridu na yanar gizo sun taya al’ummar Musulmi Murnar Sallar Idi,
Kungiyar ‘yan jaridu na yanar giz al’ummar Musulmin Najeriya murnar kammala azumin watan Ramadan tare da samun nasarar gudanar da bukukuwan karamar Sallah.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan taronta na Sallah mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban kungiyar Yakubu Salisu da mukaddashin sakataren kungiyar Abbas Yushau Yusuf, kungiyar ta bukaci al’ummar musulmi da su ci gaba da gudanar da ibadar watan Ramadan, wanda ya hada da takawa, hakuri, juriya. da taimakon mabukata.
Kungiyar mawallafan mai dauki da ’yan jarida sama da 40 da ke aiki a Kano sun sha alwashin ci gaba da kiyaye ka’idojin aikin jarida da yaki da labaran karya da ke yaduwa kamar wutar daji a Najeriya.
Kungiyar ta kuma yi kira ga sassan sadarwa na fadin kasar nan, musamman wadanda suka fara aiki da suka hada da Jami’ar Nsukka ta Nijeriya, Jami’ar Ibadan, Jami’ar Bayero Kano, da Jami’ar Maiduguri, da su hada kai da kuma Kungiyoyin dabab-daban na yan jarida a cikin gida Nigeria dama waje
kiyaye da’a na aikin jarida da sana’a yayin da duniya ke juyawa zuwa aikin jarida na kan layi ko dijital.
Har ila yau, sun bukaci masana harkokin sadarwa a fadin kasar nan da su kara ba da muhimmanci kan aikin jarida na wayar salula saboda miliyoyin mutane a yanzu suna samun bayanai da labarai a wayoyin hannu.
