News
Matasa Sun Bankawa Baburin Adaidaita Sahun Masu fashin waya Wuta A Ƙofar Famfo Kano
DAGA KABIRU BASIRU FUKATAN
Wasu fusatattun matasa sun ƙone wani Baburin Adaidaita Sahu a yankin Unguwar Ƙofar Famfo dake jahar Kano.
Matasan sun zargi masu Baburin Adaidaita sahun da yunƙurin aikata fashin waya ga wata mata, waɗanda ba su samu nasara ba.
Wakilin jaridar indaranka ya rawaito cewa Matasan dake yankin sun kawo wa matar ɗauki bayan sun hangi ƴan fashin wayar na ƙoƙarin aikata mata fashi.
hakan ce ta sanya matasan kuna wa Babur ɗin wuta har saida ya ƙone.
shafin oddity24 ya gane wa, idanunsa Baburin Adaidaita sahun yana ɗauke da nambar Karota GWL2521.
Hukumomin tsaro dai sunyi kira ga jama’a su daina ɗaukar doka a hannunsu , su bari jami’an tsaron su gudanar da bincike .
Advertisements
