Connect with us

News

Yadda Wata Mata ta Haihu a Cikin Mota

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

 

Lauya Julia Assis ta bayyana yadda haihuwar ‘yarta ta biyu ya faru, a São Paulo.
“Mata za su so haihuwa cikin gaggawa, amma babu wacce za ta so ta haihu ita kaɗai, a kan hanya, kuma a cikin mota, ba tare da taimakon likita ba,” in ji ta.

Babbar magana: waliyin amarya ya sace sadaki ana tsaka da daurin aure a Kano.

Haihuwata ta farko ta hanyar tiyata ce, amma likitoci sun shaida min cewa wannan haihuwar tawa ta biyu za ta zo cikin sauƙi saboda jikina ya riga ya saba. In ji ta.

Lokacin da na shiga ɗakin haihuwa bayan na haihu a mota, sai mutane suka tafa min.

Advertisement

Doula mahaifiya ga Julia tace “haihuwa ce irin wadda ba a taɓa samun irin ta ba.” Amma na ji tsoro sosai, na gigice, kuma na shiga cikin damuwa a kan ‘yata da mahaifiyata, wadanda suke gefena.

Duk da cewa ba a asibiti ta haihu ba, amma an yi wa jaririyar rajista kamar an haife ta ne a asibiti.

Jaridar priomnews ta rawaito cewa Ma’aikatar Lafiya ta bayyana cewa haihuwa a asibiti ita ce mafi aminci da kuma lafiya inda bayanai suka nuna cewa ita ce zaɓin kusan kashi 98% na mata.

“Lokacin da na fara jin alamun naƙuda a safiyar ranar Lahadi, ciwon ya riƙa ƙaruwa har zuwa ranar Litinin, ranar Talata ma haka, ciwon ya kasance tamkar ciwon mara a lokacin jinin al`ada.”

“A ranar Laraba da Alhamis, zafin bai ragu ba ko kadan, har na kasa jurewa, wajen karfe 4 na safe, zafin ya sake ƙaruwa sosai har na kasa kwanciya, sai na je ban-ɗaki, a nan sai na ji alamun kamar ruwa ya kusa fashewa, sai na shiga bahon wanka ko zafin da nake ji zai ragu.”

“Washe-gari sai na je asibiti, wajen likita saboda ya duba ni, da ya duba sai ya ce ruwan haihuwa ya kusan fashewa amma akwai sauran lokaci, ya ce na koma gida, bayan na koma, sai ciwon naƙudar ya ƙaru sosai, ya riƙa taso min duk bayan minti goma zuwa ashirin.

Advertisement

“Da karfe 1:37pm, na ji kamar ruwa haihuwa zai fashe kuma dama an yanke shawarar malamar jinya ce zata zo har gida ta duba ni kafin lokacin haihuwar ya yi, amma hakan bai yiwu ba saboda wajen da zata zo akwai nisa daga gida na.”

Da karfe biyu na rana, ina cikin bahon wanka yanda likita ta ce min na yi, ni kadai duk da dai mijina da mahaifiyata suna nan, zafin naƙudar sai ƙaruwa yake yi tare da alamun ruwan haihuwan ya kusa fashewa.”

“Toh, karfe biyu da rabi na kasa jure wa zafin, kawai sai na fara ihu ina kuka har malamar jinyar ta jiyo ta waya, shi ne ta ce ayi maza a kai ni asibiti.

“A hanyar zuwa asibiti, a cikin mota, sai na fara jin alamun jaririn na cuso kai har ya yi alamun fitowa, sai na fada wa mahaifiyata, shi ne a firgice ta saka hannu don ta taro jaririn, muna shiga ɓangaren haihuwa da motar, kawai sai jaririn ya fito”

“Da aka bude motar, da kaina na sauka, har na taka na zauna a kan gujerar da ake tura marasa lafiya, tare ta jaririyata a hannuna, mahaifiyata kuma duk fuskanta cike da tsoro da gigicewa.

Sa’o’i kadan bayan haihuwar, likitocin sun gano cewa Julia na fama da zubar jini, wanda sai da aka yi mata ƙarin jini leda biyu, amma ta warke cikin mako guda.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending