News
Yan matan Zamfara sun sake samun ‘yanci bayan watanni bakwai da aka yi garkuwa da su
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta karbi ‘yan mata hudu da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a watan Janairu bayan da masu garkuwa da su suka sako su.
‘Yan matan: Jamila Isa, Aisha Isa, Ummulkhairi Musa da UmmulKhairi Umar, an sace su ne a hanyar Kaura Namoda zuwa Birnin Magaji.
Gwamnatin jihar da iyalan ‘yan matan ba su bayyana ko an biya kudin fansa ba kafin a sako ‘yan matan.
PREMIUM TIMES ta rawaito cewa jami’an hukumar SSS ne suka kawo ‘yan matan babban birnin jihar, Gusau.
Sanarwar da Sulaiman idris, mai magana da yawun gwamnan Zamfara ya fitar, ta ce an ceto ‘yan matan ne ta hanyar “sa hannun gwamnati”.
Gwamnatin jihar ta ce ta damu bayan ta samu wani faifan bidiyo da ke nuna ‘yan matan da aka yi garkuwa da su suna rokon iyalansu da gwamnati da ta kawo musu dauki.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke fama da munanan ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma. Mutane da dama da aka sace har yanzu suna cikin sansanonin ‘yan ta’adda da suka bazu a fadin jihar.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
