Connect with us

News

Kungiyar Kwadago Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta sake gayyatar kungiyar kwadago ta kasa (NLC) don yin wata ganawa kan yajin aikin da ta ke shirin yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Simon Lalong, ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya fitar.

Wani bawan Allah ya Gwnagwaje Auwalu Salihu da Sabon Adaidaita Sahu.

Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Lalong a ranar 4 ga watan Satumba ya gayyaci NLC da kungiyar kwadago ta kasa (TUC) don yin wata ganawa da nufin dakile yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka fara yi a fadin kasar.

Advertisement

Jatidar Inda Ranka ta kuma ruwaito cewa TUC ce kadai ta halarci taron.
Lalong ya ce ya umurci ma’aikatar kula da ayyukan kungiyoyin kwadago da hulda da masana’antu da ta kira taron da shugabannin kungiyar ta NLC ranar Litinin.

Ya ce yana da kyau kungiyoyin kwadago su zauna da gwamnati domin warware duk wasu batutuwan da ke gabansu domin kaucewa ci gaba da kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.

Advertisement

“Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu za ta rika shiga cikin kungiyoyin kwadago da kuma amsa matsalolinsu bayan tuntubar juna da tattaunawa.

Lalong ya ce “Wannan don tabbatar da daidaiton masana’antu wanda ke da matukar muhimmanci ga ci gaban Ajandar Sabunta Fata.”

Advertisement

Haka kuma, a ranar 1 ga watan Satumba ne majalisar zartaswar kungiyar NLC ta kasa, a cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi barazanar shiga yajin aiki na tsawon kwanaki 21.

Haka kuma Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa NLC ta bukaci gwamnati ta kara mafi karancin albashin ma’aikata zuwa N200,000 da sauran bukatun da ta gabatar.

Advertisement

Wani labarin kuma Wani bawan Allah ya Gwnagwaje Auwalu Salihu da Sabon Adaidaita Sahu.

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

Advertisement

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

 

Advertisement

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending