Connect with us

News

Rundunar Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Published

on

Rundunar sojajin najeriya

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Rundunar Sojoji na musamman na rundunar hadin guiwa da ke aiki a shiyyar Arewa maso Yamma a karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Kasar nan, sun sake ceto wasu mutane 15 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Advertisement

An ceto mutanen ne a ranar Litinin, 25 ga Satumba, 2023, a kauyen Kayan Boggo da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar.

Korar da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano ta yi, ta bawa ‘yan Najeriya da dama mamaki.

A cewar Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, ya ce, bayan samun bayanan sirri, sojojin sun tare wata hanya da ake zargin ‘yan ta’addan na amfani da ita in sun sato mutane.

Advertisement

Ya ce, “sojojin sun kashe ‘yan ta’addan da dama da suka fada tarkonsu, lamarin da ya tilasta musu tserewa suka bar mutanen da suka sato”.

“Majiyoyin soji sun ce, an mika wadanda aka tsiratar ga hakimin Gwashi domin hada su da iyalansu.”

Advertisement

A baya LEADERSHIP ta rahoto cewa, an kubutar da dalibai mata 13 cikin sama da 20 na Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS), wadanda ‘yan bindiga suka sace a wani dakin kwanan dalibai da ke garin Sabon Gida a karamar hukumar Bungudu ta jihar a ranar Juma’a.

Wani labarin kumaGwamnan jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya yi alhinin rasuwar Barista Halliru Danga Maigari

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Advertisement

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending