News
Ba ma tattaunawar sulhu da ‘yan bindigar Jahar Zamfara: Tinubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarraya ta musanta zargin da gwamnan Jihar Zamfara ya yi cewa tana tattaunawa da ‘yan bindiga da ke addabar jihar.
Ministan Watsa Labarai na kasar Mohammed Idris ne ya bayyana haka ranar Litinin a sanarwar da mataimakin darakta a ma’aikatarsa ya fitar.
Rundunar Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta mayar da martani ne kan zargin da gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya yi cewa tana neman sulhu da ‘yan bindiga da suka kwashe shekara da shekaru suna kashewa tare da sace mutane a jiharsa.
“Ba tare da wata tantama ba, minista yana sanar da cewa babu wani jami’in gwamnatin tarayya da ke yin sulhu da dan bindiga ko kungiyar ‘yan bindiga. Sai dai gwamnati na ci gaba da tsayawa a matsayinta cewa tana neman duk wata hanya da za ta hana watsuwar zaman dar-dar da kuma dawo da zaman lafiya ga al’ummar da ‘yan bindiga suka addaba,” in ji sanarwar.
Zan bai wa masu cewa ba zan iya Ministan Tsaro ba kunya: Matawalle
Hakan na faruwa ne kwanaki kadan bayan ‘yan bindiga sun sace wasu daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, lamarin da ya jawo mummunar suka daga wurin ‘yan kasar, ko da yake an kubutar da wasu daga cikinsu kuma gwamnati ta ce tana yin bakin kokarinta domin ceto sauran.
Ministan ya bayyana takaicinsa game da yadda gwamnan jihar ya siyasantar da batun tsaro, yana mai cewa “maimakon (gwamnan) ya yaba wa jami’an tsaro da gwamnatin tarayya bisa kubutar da daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusai, ya zabi ya siyasantar da al’amari mai sarkakiya domin cin ribar siyasa”.
Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga wadanda ke sace dalibai da mutanen gari suna neman kudin fansa. Sannan a lokuta da dama suna kashe wadanda suka sace.
Wani labarin kumaRundunar Sojoji Sun Ceto Wasu Mutane 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
