Connect with us

News

An Kori Karen Joe Biden Daga fadar gwamnatin kasar ta White House Saboda Yawan Cizon Mutane

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

An fitar da karen Shugaban Amurka, Joe Biden, daga fadar gwamnatin kasar ta White House saboda yadda yake yawan cizon mutane.

Mai magana da yawun uwargidan shugaban, Jill Bide, wato Elizabeth Alexander, ta ce daukar matakin ya biyo bayan yadda karen mai suna “Commander” ya ciji wani ma’aikacin fadar da kuma wasu ma’aikatan hukumar leken asirin kasar.

Bankin Duniya ya ce kudin Nijeriya yana cikin kudaden Afirkan da darajasu ta ragu

Elizabeth, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ta ce shugaban da maidakinsa sun damu matuka da lafiyar ma’aikatan da kuma jami’an tsaron da suke kula da su.

 

Advertisement

“Yanzu haka Commander ba ya cikin fadar, a daidai lokacin da ake ci gaba da nazari a kan mataki na gaba da za a dauka.

“Biden da maidakinsa suna matukar godiya saboda hakuri da goyon bayan da Hukumar Leken Asirin Amurka da dukkan wadanda abin ya shafa suka nuna, yayin da suke ci gaba da kokarin lalubo bakin zaren,” in ji Elizabeth.

Sai dai ba ta bayyana inda aka kai karen ba mai shekara biyu, wanda aka horar a kasar Jamus, sannan ba ta fadi ko matakin na wucin gadi ne ko kuma na dindindin ba.

Tun ranar Asabar din da ta gabata dai rabon da a ga karen, inda a ranar aka hange shi a saman wani ginin da shugaban yake zama.

A Wani labarin kuma Bankin Duniya ya ce kudin Nijeriya yana cikin kudaden Afirkan da darajasu ta ragu

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

 

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

 

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

 

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending