News
Ma’aikatan Hukumar Kwashe Shara ta Kano Sun Gudanar Da Zanga-zanga Kan Rashin Biyan Su Hakkokin Su
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu ma’aikatan hukumar kwashe shara ta jahar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana da safiyar Litinin 9 ga watan Oktoba 2023, kan rashin biyan su hakkokinsu na watanni 5 tun da sabuwar gwamnatin jahar Kanon ta kama aiki.
Masu korafin dai sun zargi shugaban hukumar kwashe sharar ta jahar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago da yiwa gwamnatin jahar Kanon zagon kasa , wajen rashin bayyana wa gwanatin matsalolin da suke fuskanta inda suka bukaci gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya sauya musu shugaban hukumar.
Wasu daga cikin masu sharar sun sahida wa kafar Jaridar Inda Ranka cewa, tun abaya sun nemi a biya su hakkokin nasu hakan baiyuwu ba, tare da bayyana musu cewa suje su ci gaba da yin aikin su.
Kungiyar Health Special Reporters ta Zabi Shafa’atu Said Karaye a matsayin shugabar kungiyar
Talatu Adamu daya daga cikin masu korafin ta ce, tana bin tsohuwar gwamnatin jahar Kano lokacin Dr. Abdullahi Umar Ganduje watanni 3, yayin da ta ke bin sabuwar gwmanatin Engr. Abba Kabir Yusuf watanni 5.
ma’aikatan sunce kullum sune suke tsaftace titinan jahar Kano tun sanin sanyin safiya , duk da hatsarin da yake fuskantar su na zirga-zirgar ababen hawa akan tituna.
Aminu Abubakar Ahmad ya shaida wa oddity24 cewa, kafin tsohuwar gwamnati ta sauka babu hukumar domin an rush eta, amma bayan zuwan sabuwar gwamnatin jahar Kanon ta dawo da hukmar, kuma an tantance su har aka barsu su ci gaba da yin aikin amma tsawon watanni biyar ba a yasu ba.
Masu zanga-zangar sun zargi shugaban hukumar yin buris da biyan hakkokinsu , domin sunce a tantance har sau uku amma shuru babu labarin komai kuma suna ci gaba zuwa wajen aikin su a kullum.
Sai dai duk kokarin jin ta bakin shugaban hukumar Alhaji Ahmadu Haruna Zago , lamarin ya ci tura sakamakon jami’an tsaro sun garkame kofar shiga hukumar tare da hana shiga da fita baki daya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
