News
Wani Saurayi Da Budurwa Sun Daurawa Kansu Aure A Jahar Jigawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu matasa sun daurawa abokinsu aure da budurwarsa ba tare da sanin iyayensu ba. Wannan al’amari mai kama da al’amara ya faru ne a unugwar Gandun Sarki cikin karamar hukumar Mallam Madori a jihar Jigawa.
Matashin mai suna Yahaya Isa wanda aka fi sani da Badi, kamar da wasa yace idan budurwar ta amince su yi aure yanzu ma ga sadaki a hannunsa.
Hukumar REA Tace Bata ɓata Lokacin Ba Wajen Magance Matsalolin Da suka shafi Tsare-Tsaren Hukumar
Nan take kuwa budurwar mai suna Sa’a ta ce, ta amince su yi aure. Anan ne abokai suka hadu aka daura auren har ma aka bayar da sadakin N15,000 da zimmar za a ciko N35,000 a matsayin kudin sadaki.
Leadership ta rawaito cewa Sheik Yusuf Abdurrahman, Limamin masarautar Hadejia na daga cikin malaman addinin da suka bada fatawar cewa aure ya dauru.
A wani labarin kuma Hukumar REA Tace Bata ɓata Lokacin Ba Wajen Magance Matsalolin Da suka shafi Tsare-Tsaren Hukumar
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
