News
Hadarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 11 A Jihar Jigawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Akalla mutane 11 ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Kwanar Gujungu da ke jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiitu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.
Reshen matasan liman kano na 2 gwani muhamnad zahraddin ke gayyatar daukacin zuri’ar taron su
Ya ce hatsarin ya afku ne a ranar Asabar din da ta gabata inda wata mota kirar Honda LE da wata karamar mota kirar Golf ta yi karo da juna a sakamakon haka, dukkan mutane 11 da ke cikin motocin biyu sun rasa rayukansu a nan take.
Punch ta ruwaito cewa tawagar ‘yan sanda daga sashin kula da zirga-zirgar ababen hawa, hedkwatar ‘yan sanda ta Taura, sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai gawarwakin zuwa babban asibitin, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsu,” inji shi.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda AT Abdullahi, a madadin ‘yan sandan ya jajantawa iyalan mamatan tare da addu’ar Allah ya gafarta musu kurakurensu.
A wani labarin kuma Reshen matasan liman kano na 2 gwani muhamnad zahraddin ke gayyatar daukacin zuri’ar taron su
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
