News
Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukunci akan zaɓen Nasarawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun ƙoli ta ce za ta sanar da ranar da za ta raba gardama a ƙarar da David Ombugadu na jam’iyyar PDP ya ɗaukaka domin ƙalubalantar nasarar gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
A ranar Talata ne kotu ƙarƙashin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci a ƙarar.
A shekarar da ta gabata, hukumar zaɓe INEC ta ayyana Sule a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.
Sule ya samu ƙuri’u 347,209 inda ya doke abokin karawarsa na PDP Ombugadu wanda ya samu 283,016.
Sakamakon zaɓen da bai yi masa daɗi ba ne ya sa ɗan takarar na PDP ya je kotun ƙararrakin zaɓe don ƙalubalantar matakin INEC na ayyana Sule a matsayin wanda ya yi nasara.
Wata bakwai bayan nan, kotun ta soke nasarar Sule inda ta ayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.
Hakan ya sa gwamna Sule ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara a Abuja wadda ta soke hukuncin kotun ƙararrakin zaɓen inda ta sake ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.
A yau ɗin ne kuma, Kotun ƙolin ta ɗauki irin wannan matakin kan ƙarar da ɗan takarar gwamna a zaɓen Kebbi, Manjo Janar Aminu Bande na PDP ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Nasir Idris na APC a matsayin gwamnan jihar.
