News
Yadda ‘Yan Bindiga Suka Sace Mahalarta Ɗaurin Aure 55, Da Kashe Mutane 3
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kan ayarin motocin daurin aure a garin Damari da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, inda suka kashe wasu mutane uku tare da yin awon gaba da baki ‘yan daurin aure su kusan 55.
Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis a garin Damari kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar da faruwar haka ranar Juma’a, kamar yadda kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito.
Bakin daurin auren wadanda ke cikin motocin rakiyar amarya zuwa gidanta, suna cikin wata budaddiyar motar kurkura a lokacin da ‘yan ta’addar suka afka musu.
Wata majiya ta bayyana cewa mutanen da harin ya ritsa da su sun haura mutum 70, inda da dama wasu daga cikin su suka yi nasarar tserewa daga motar lokacin ya yin harin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
