News
Mun janye kalamanmu tare da bai wa Nuhu Ribadu hakuri —Gwamnatin Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Kano ta ba wa Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu hakuri kan zargin hannunsa a rikicin masarautun jihar.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam a ranar Asabar yana zargi Ribadu da yunkurin dawo da Alhaji Aminu Ado Bayero kan kujerar Sarkin Kano bayan gwamnatin jihar ta sauke shi tare da sauran sarakunan jihar.
Mataimakin gwamnan Jahar Kano komarade aminu abdussalam ya Nemi afuwar Shugaban sojoji nuhu rubado
Daga bisani Ribadu ya nesanta kansa da kuma ofishinsa daga rikicin, sannan ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu.
Bayan haka ne mataimakin gwamnan ya ba da hakuri ga Ribadu yana mai cewa yaudarar gwamnatin aka yi da bayanan da aka ba ta.
“Mun kara zurfafa bincike inda kuma gano cewa yaudarar mu aka yi, saboda haka, a madadin gwamnatin Kano, mana ba da hakuri ga Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro,” in ji mataimakin gwamnan.
Gwamnatin jihar ta kuma bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki kada abin ya kara rincabewa fiye da haka.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
