Connect with us

News

Kano :Ana Fargabar Mutuwar Masu Zanga Zanga Da Dama A Unguwar Kurna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Duk da dokar hana fita ta awanni 24 a jihar Kano, Masu zanga zanga a jihar sun zargi jami’an tsaro da harbi kan masu zanga zanga a Unguwar Kurna yau Asabar.

Advertisement

Ta cikin wata ganawa da jaridar INDA RANKA ta yi wani mazaunin yankin  kuma guda cikin masu zanga zangar Kwamared Usman Bandiro. yace sun fito zanga-zangar ta lumana amma wasu cikin jami’an ‘yan sandan dake aiki domin samar da tsaro suka fara harba musu hayaki mai saka hawaye inda daga bisani kuma suka fara harbin su da bindiga.

Kaso 75 Cikin 100 Na Yan Arewacin Yan Najeriya Basa Iya Cin Abinci Sau Uku A Rana —Gwamna Uba Sani

Badirawo ya ce muddin aka cigaba da tafiya a haka baiga  dalilin dazai  saka su koma gida ba har sai gwamnati tayi musu abinda ya kamata, na dawo da tallafin man fetur da magance tsadar rayuwar a fadin Nijeriya.

Advertisement

Ana fargabar an harbi mutum sama da Goma cikin masu zanga-zangar

Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga zangar na dauke da kwalaye da aka rubuta korafe korafensu daban-daban.

Advertisement

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar hana fita ta awanni 24 bayan bata gari sun kutsa cikin masu zanga-zanga.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending