Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Fasinjoji Da Dama  A Hanyar Gusau Zuwa Funtua 

Published

on

Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji a hanyar Gusau Funtua

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Ƴan bindiga a wani karon sun sake tare hanyar Gusau-Funtua tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a motoci uku a kusa da ƙauyen Margazu a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Advertisement

Blueprint ta ruwaito cewa Hallau, ƴan bindigar sun tare hanyar a mabanbanta wurare ciki har da unguwan Chida da makusanta garuruwa inda suka tare motoci biyar da yin garkuwa da fasinjoji.

Ba Mu Sanya Farashin Man Fetur Ba – Matatar Man Dangote

Mazauna yankunan sun ce wasu ƴan bindigar cikin waɗanda aka kashe sun jima su na addabar yankin ta hanyar amfani da lokacin damina wajen kai hare-hare.

Advertisement

Wani daga cikin su ya ce, su kan kawo hari kusan kullum tare da yin garkuwa da masu zirga-zirga a hanyar.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an baza sojoji don farautar ƴan bindigar tare da samar da tsaro a yankunan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending