News
NLC Ta Umurci Mambobinta Da Su Tsunduma Yajin Aiki A Duk Jihar Da Aka Ki Biyan Mafi Karancin Albashi
Kungiyar Kwadago ta NLC a Najeriya ta umurci ya’yanta da su tsunduma yajin aiki a duk jihar da aka ki biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi daga ranar 1 ga watan Disamba 2024
Wannan umarnin ya biyo bayan kudurorin da kungiyar NLC ta gudanar a taron majalisar zartarwa ta kasa a karshen mako.
Kungiyar ta lura da jinkiri da kuma kin amincewa da wasu gwamnatocin jihohi suka yi na aiwatar da dokar mafi karancin albashi ta kasa ta shakarar 2024.
Wannan rashin mutunta doka ne da kuma rayukan miliyoyin ma’aikatan Najeriya
Haka zalika Kungiyar ta kuduri aniyar kafa kwamitin aiwatar da mafi karancin albashi na kasa wanda zai fara aikin tantancewa, wayar da wayar da kan jama’a a fadin kasar nan.
“Don haka, an umurci mambobinta da su tsunduma yajin aiki a duk jihar da aka ki biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi daga ranar 1 ga watan Disamba 2024
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
