Connect with us

News

Fursunoni Sama Da Dubu 6 Sun Tsere Daga Kurkuku

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rahotanni daga Mozambique na cewa adadin fursunoni da suka tsare a wani gidan yarin ƙasar ya haura dubu 6000 ciki harda wasu manyan ƴan ta’adda.

Advertisement

Tun farko dai muhukuntan Mozambique bayyana tserewar fursunoni 1,500 a gidan yarin dake kusa da babban birnin ƙasar Maputo a ranar kirsimeti, sai dai rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa sama da fursuninu dubu 6 ne suka tsere bayan barkewar tarzomar da ya kai ga hallaka mutane 33.

An Samu Mace Ta Farko Da Ta Zama Kwamishinar Ƴan Sanda A Kano

Fursunonin sun yi amfani da tarzomar da ta barke sakamkon zanga-zangar da magoya bayan jam’iyyun adawa ke yi bayan tabbatar da nasarar jam’iyyar Frelimo mai mulki a zaben watan Oktoba.

Advertisement

Shugaban ƴan sandan ƙasar Bernardino Rafael, ya ce fursunoni sun kwace makamai daga hannun masu gadinsu tare sako sauran ƴan uwansu, ciki harda ƴan ta’adda 29 dake zaman wakafi, wanda ya ce abin damuwa ne.

Jami’in ya ce masu zanga-zangar sun yi tattaki har kusa da gidan yarin, tare da lalata motocin ƴan sanda da tashoshi da ababen more rayuwa bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da jam’iyyar Frelimo mai mulki a matsayin wadda ta lashe zaɓen ranar 9 ga Oktoba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending