News
Gwamnatin Bauchi Ta Ware Miliyan 400 Don Sayen Computer 6 A Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ware Naira miliyan 400 a cikin kasafin kudin shekarar 2025 don sayen kwamfuta guda shida domin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar.
JARIDAR THE GUARDIAN ta rawaito cewa, haka kuma, gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan daya don “sayen fili domin gina ofisoshi da gine-gine.” Za ta kuma kashe Naira miliyan 170 don sayen janareta domin samar da wutar lantarki a ofishin SSG.
Yan Sanda Sun Kama Wata Mota Ɗauke Da Ƙananan Yara 59 Da Ake Zargin Sato Su Aka Yi
Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Ibrahim Musa, ya soki wannan kasafi, yana mai bayyana shi a matsayin rashin fifikon abubuwan da suka dace a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da wahalhalu sakamakon manufofin tattalin arzikin gwamnati.
Ya ce: “Kowa zai yi imani cewa ajiye kudi zai fara ne daga matakai daban-daban na gwamnati, amma abin da ake gani ya saba hakan. Mun ga alkaluman da aka kara na kashe kudin ayyukan ci gaba daga wannan gwamnati.
“Gwamnatin jihar na kira ga ‘yan kasa su yi hakuri ta hanyar canza yanayin rayuwarsu. A gefe guda kuma.
Ta yaya za ka shawo kan mutumin da ba shi da abinci a kan teburinsa cewa za ka sayi kwamfuta shida da kudin Naira miliyan 400?
“Wannan adadi na iya gina cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda shida inda za a kai ayyukan kiwon lafiya kusa da ‘yan Najeriya. Wannan shi ne abin da gwamnati ke saya kowace shekara kuma ya zama al’ada.”
Musa ya bukaci Gwamnatin Jihar Bauchi da ta kauce wa yin hakan tare da mayar da hankali kan ayyukan da za su kawo ci gaba a rayuwar al’ummar jihar.
