Connect with us

News

Rashin Tsaro: Mutum 91,740 Suka Rasa Rayukasu A Najeriya Cikin Shekaru 13 – Rahoto

Published

on

AFGHANISTAN UNREST TALIBAN

 

Wani sabon rahoto da aka gabatar a Abuja ya bayyana cewa, akalla mutum 91,740 sun rasa rayukansu sakamakon matsalar rashin tsaro a Najeriya tsakanin shekarun 2011 zuwa 2024.

Advertisement

Rahoton mai shafuka 95 da aka fitar karkashin shirin INSPIRES tare da hadin gwiwar Kimpact Development Initiative (KDI), Dataphyte da Spaces for Change, ya nuna cewa gazawar gwamnati wajen magance matsalolin tattalin arziki, kabilanci da rashin shugabanci na gari ne suka haddasa wannan matsala.

NANS Zata Yi Zanga-zanga Kan Rufe Makarantun Boko A Wasu Jihohin Arewa Saboda Azumin Ramadan

A cewar shugaban bincike na KDI, Mr Oluwafemi Adebayo, shekarar 2014 ce ta fi yawan asarar rayuka, inda aka yi asarar mutum 14,470 sakamakon hare-haren Boko Haram da rikice-rikicen kabilanci.

Advertisement

Rahoton ya bayyana cewa daga 2020 zuwa 2022, an samu karancin ‘yancin fadin albarkacin baki da gudanar da zanga-zanga, musamman bayan zanga-zangar #EndSARS.

Jihohin da aka fi samun matsalar rashin tsaro sun hada da Borno, Kaduna, Zamfara ,Benue ,Plateau

Advertisement

Sai dai rahoton ya bayyana Jigawa, Ekiti, Osun, Abia, da Kwara a matsayin jihohi mafi aminci a Najeriya cikin shekaru 13 da suka gabata.

Rahoton ya bukaci gwamnati da ta samar da manufofin tsaro da ke da fifikon kare rayukan jama’a tare da tabbatar da ‘yancin fadin albarkacin baki ba tare da takura wa al’umma ba.

Advertisement

Idan ba a dauki matakan gaggawa ba, rahoton ya yi hasashen cewa zuwa shekara ta 2029, yawan take hakkin dan Adam na iya kaiwa 1,846 a duk fadin kasar.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending