Connect with us

News

Martanin Kwankwaso Kan Dokar Ta-Baci a Rivers Ya Jawo Cece-Kuce

Published

on

Kalaman tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kan dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa a Jihar Rivers sun haddasa cece-kuce a fadin Najeriya.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya soki ‘yan majalisar wakilai da suka amince da matakin, yana masu lakabi da “’yan amshin Shata.” Ya bayyana matakin a matsayin abin kunya da barazana ga dimokuradiyya.

Advertisement

Yan Daba Sun Kashe Matashi Mai Shekaru 23 A Masallaci A Kaduna

Sanatan ya kuma caccaki Shugaba Tinubu, yana mai cewa dakatar da gwamnan farar hula tamkar gayyato sojoji ne, sabanin kokarin da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya yi na mayar da su bariki.

Wasu ‘yan Najeriya sun yi mamakin yadda har ‘yan majalisar da ke goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya suka yi shiru a yayin muhawarar dokar ta-bacin, lamarin da wasu ke ganin kamar sun saba wa ra’ayin jagoransu.

Advertisement

Sai dai Honorabul Garba Diso, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwale, ya ce abin da suka kalla shi ne maslahar Jihar Rivers da kokarin tabbatar da zaman lafiya.

Akwai kuma zargin cewa an yi amfani da kudi wajen saye wasu ‘yan majalisu don tabbatar da dokar ta-bacin, zargin da har yanzu ba a samu martani daga wasu ‘yan majalisar Kano ba.

Advertisement

Matakin dai na ci gaba da jawo muhawara tsakanin ‘yan siyasa da jama’a, inda wasu ke goyon bayansa, yayin da wasu ke ganin hakan barazana ce ga tafiyar dimokuradiyya a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending