News
Matan Kogi Sun Fito Don Nuna Damuwa Kan Yawaitar Garkuwa da Mutane
Mazauna kauyen Oke-Ere da ke karamar hukumar Yagba West a Jihar Kogi sun fito kan titi a ranar Litinin don nuna rashin amincewarsu da yawaitar garkuwa da mutane da koma bayan tsaro a yankin.
Wasu daga cikin al’ummar sun bayyana wa jaridar Leadership cewa lamarin ya zama ruwan dare, inda ake samun sace-sace da garkuwa da mutane akai-akai, wanda hakan ya sanya su cikin tsoro da firgici.
SATAR KAYAN MAKARANTU: Hukumar NSCDC Ta Kama Mutane Biyar A Kano
Wani mazaunin da ya ba da rahoton amma bai ga damar bayyana sunansa ba, ya ce wani da ake zargin dan garkuwa da mutane ya fito fili ya yi ikirarin tuba, inda ya fallasa wasu ‘yan asalin kauyen da ke hannu a wadannan ayyukan.
Hakan ya haifar da fushin matan kauyen, wadanda suka fito kan titi suna kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa don dakile wadannan ayyukan.
Duk da haka, shugaban karamar hukumar Yagba West, Hon. Tosin Olokun, ya musanta cewa taron matan ya shafi garkuwa da mutane. A cewarsa, irin wannan taron na shekara-shekara ne, wanda ake yi domin yin addu’a da gargadin masu kawo hargitsi a yankin.
A wata hira da aka yi da Hon. Femi Adeyeye, kwamishinan ayyuka na musamman da ilimi a karamar hukumar, ya tabbatar da cewa taron ya samu izini daga masarautar Elere da kuma hukumar karamar hukumar.
“Wannan ba zanga-zanga ba ce, sai dai taruwar mata domin yin addu’a da kuma Allah-wadai da duk wanda ke kawo tashin hankali ga al’umma,” in ji shi.
Duk da haka, rahotanni daga yankin sun nuna cewa garkuwa da mutane da sauran laifuka sun karu a sassan Kogi West. A watan da ya gabata, al’ummar Oduape da ke karamar hukumar Kabba Bunu ma sun gudanar da zanga-zanga irin ta Oke-Ere, inda suka nemi gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakan gaggawa.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
