Connect with us

News

Pakistan Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Yayin Da Rikici Da Indiya Ke Kara Tsananta

Published

on

61041341 803

Pakistan ta ce ta yi nasarar gwajin wani sabon makami mai linzami a daidai lokacin da ake fama da karin rashin jituwa tsakaninta da makwabciyarta Indiya.

Rundunar sojin kasar ta ce makamin linzamin ya yi tafiyar kusan kilomita 450 daga inda aka harba shi, kuma gwajin wani bangare ne na aikin tabbatar da lafiyar makamansu da kuma ingancin aikin sojin kasar.

2027: Ana Zargin Wike Da Gwamnonin PDP Sun Cimma Yarjejeniya

Gwamnatin Islamabad ta ce wannan mataki ne da ke nuna shirin dakarunta wajen kare iyakokin kasar da kuma nuna karfi a lokacin da ake fama da kalubale a yankin.

Gwajin ya biyo bayan wani hari da ya kashe ’yan yawon bude ido na Indiya a garin Pahalgam da ke yankin Kashmir a ranar 22 ga watan jiya.

Indiya ta dora laifin kisan kan Pakistan, zargin da ita kuwa Pakistan ta musanta, tana mai cewa ba ta da hannu a lamarin.

Har yanzu ba a ji wani martani daga bangaren Indiya game da harba makamin ba.

Advertisement

 

 

DW

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending