News
Majalisar Dattawa Ta Gabatar Da Kudurori 844 Cikin Shekaru Biyu – Inji Akpabio
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Majalisar Dattawa ta 10 ta karɓi da kuma gabatar da ƙudurin dokoki guda 844 tun bayan da aka rantsar da ita zuwa yanzu.
Sanata Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin wani zama na haɗin gwiwa da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ‘yan majalisar tarayya, a matsayin wani ɓangare na shagulgulan Ranar Dimokuraɗiyya da aka gudanar a zauren Majalisar Tarayya, Abuja.
Sojoji Sunyi Ajalin Ɗan Auta Tare Da Ƙarin Wasu Ƴan Bindigar A Zamfara
Taron dai ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC da kuma wasu tsofaffi da ‘yan majalisar da ke kan mukami a yanzu.
A cikin jawabinsa, Sanata Akpabio ya bukaci Shugaban Ƙasa da ya duba yiwuwar kafa wani gidan tarihin Ranar 12 ga Yuni — domin tunawa da muhimmancin wannan rana a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya, musamman ma dangane da zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1993 da ake kallon mafi sahihanci a tarihin ƙasar.
Ya ce, “Idan gwamnati na tafiya cikin haɗin kai, babu shakka cigaba yana samuwa.”
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
