Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Richarlison, Dybala, Melo, Cavani, Osimhen, Porozo, Henderson
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Manchester United tana son sayen dan wasan gaban Everton da Brazil Richarlison. Ana rade radin dan wasan zai tafi Real Madrid, wadda tsohon abokinsa Carlo Ancelotti yake jagoranta. (Goal.com)
Juventus ta tabbatar cewa Paulo Dybala zai bar kungiyar a bazara. A baya an ce Manchester United da Tottenham sun yi zawarcin dan kasar Argentina mai shekara 28. (Fabrizio Romano)
Newcastle za ta koma neman dan wasan Napoli Victor Osimhen, duk da cewa rahotannin sun nuna cewa kungiyar ta kasar Italiya ta ki amincewa da tayin £100m da Magpies suka mika mata kan dan kasar Najeriya mai shekara 23 a watan Janairu. (Express)
Mauricio Pochettino, Erik ten Hag, Julen Lopetegui da Luis Enrique na gaba-gaba a cikin mutanen da ake duba yiwuwar dauka a matsayin kocin Manchester United a yayin da kungiyar ke neman kocin dindindin da zai maye gurbin Ralf Rangnick a bazara. (Sky Sports)
Arsenal za ta nemi daukar Arthur Melo, mai shekara 25, daga Juventus a bazara bayan ta gaza cimma yarjejeniya da dan wasan na Brazil a watan Janairu. (Calciomercato, in Italian).
Inter Milan tana so dan wasan Manchester United da Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 35, ya maye gurbin dan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekaru 33. (Mail, via Gazetta dello Sport)
Arsenal da Liverpool suna sanya ido kan dan wasan PSV Eindhoven Cody Gakpo, mai shekara 22, sai dai za su fuskanci gogayya daga Barcelona da Bayern Munich. (Express via The Athletic, subscription required)
Manchester City na shirin mika bukatarsu ta daukar dan wasan Boavista mai shekara 21 dan kasar Ecuado Jackson Porozo. (Ojogo, in Portuguese)
Leeds United na sha’awar kyaftin din Trabzonspor kuma golan Turkiyya Ugurcan Cakir, mai shekara 25, kuma za ta kalli fafatawar da zai yi da Portugal ranar Alhamis a wasan neman samun gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya. (Fanatik, in Turkish)
Arsenal na son tsawaita kwangilar Bukayo Saka domin hana wasu kungiyoyin Premier League neman dan wasan na Ingila mai shekara 20. (The Athletic, subscription required).
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
