News
’Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Sarkin Shuwaka Bayan Garkuwa Da Shi A Filato
’Yan bindiga sun kashe Sarkin Shuwaka na Garga, a karamar hukumar Kanam ta Jihar Filato, Malam Hudu Barau, kwanaki shida bayan sun yi garkuwa da shi. An gano gawarsa a cikin dajin Wanka.
Kungiyar Cigaban Kanam (KADA) ce ta tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da shugabanta, Shehu Kanam, da sakataren ta, Barrister Garba Aliyu, suka fitar a ranar Litinin. Kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da kuma tunatarwa kan yadda matsalar tsaro ta yi kamari a yankin.
Sai Ka Kalli Tallace-Tallace Kafin Ka Samu Takardar Bayan Gida A China
KADA ta soki gwamnati a matakai daban-daban da cewa ta kasa daukar matakan gaggawa duk da rokon da al’umma ke ta yi na kawo karshen hare-hare, garkuwa da mutane da kisan gilla. Ta ce jama’ar Garga da makwabtansu na rayuwa cikin fargaba.
Kungiyar ta yi kira ga Gwamna Caleb Mutfwang da ya ayyana dokar ta baci a yankin tare da tura jami’an tsaro yadda ya kamata.
Haka kuma ta zargi wakilan majalisar jiha da na tarayya daga yankin da gazawa wajen kare jama’arsu daga hare-haren ’yan bindiga.
