News
Jami’an ‘Yan Sandan Nijeriya Sun Kwato Motoci Biyu Da Aka Sato Daga Netherlands
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta samu nasarar kwato wasu motoci biyu na alfarma da aka sato daga ƙasar Netherlands aka shigar da su cikin ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, hukumar ‘yan sanda ta duniya ta INTERPOL ce ta jagoranci wannan bincike tare da haɗin gwiwar sashen hulɗa da ƙasashen waje na rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Kotu bata da ikon Tilasta Auren Mai Wushirya da ‘Yar Guda – Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya
Motocin da aka kwato sun haɗa da Toyota C-HR 2020 da kuma Toyota RAV4 2019, waɗanda aka gano a wurare daban-daban a jihohin Legas da Akwa Ibom.
Rahoton bincike ya nuna cewa an sato motocin ne daga Amsterdam da Midden-Nederland, sannan aka shigar da su Nijeriya ta jirgin ruwa a ƙarshen shekarar 2023.
Kakakin rundunar, ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a safarar motocin da kuma hanyoyin da ake bi wajen shigar da irin waɗannan motoci cikin ƙasar.
TRT GLOBAL
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
