News
Jami’an DSS Sun Kama Likitan Da Ake Zargi Yana Kula Da ‘Yan Bindiga A Daji
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wani likita a Jebba, Jihar Kwara, bisa zargin yana ba ’yan bindiga magunguna. Ana zargin likitan da jigilar kayan jinya daga Jihar Sakkwato zuwa dazuzzukan da ’yan bindiga ke boye domin kula da wadanda suka jikkata.
A cewar DSS, cafken likitan ya biyo bayan bayanan sirri da suka sama. Kakakin Gwamnan Kwara, Rafiu Ajakaye, ya ce an kama likitan ne a Jebba bayan samun sahihan bayanai kan ayyukan ’yan bindiga da masu safarar kayan jinya.
Gwamnatin Kano Ta Ce Yin Goyo Da Sunan Achaba Kawai Aka Hana A Fadin jihar
Jami’an tsaro sun ce: “Kungiyoyin miyagun suna bukatar kulawar likitoci saboda raunuka da suka samu yayin artabu da jami’an tsaro.
Jihar Kwara ta sha fama da hare-haren ’yan bindiga. A watan Nuwamba, an sace mutane 38 a Eruku, inda wasu uku suka mutu. Haka zalika, wani manomi an sace shi a kan hanyar Eruku–Koro.
